15 December 2007 15 December 2007 15 December 2007 بعثه مقام معظم رهبری در گپ بعثه مقام معظم رهبری در سروش بعثه مقام معظم رهبری در بله
15 December 2007 15 December 2007 15 December 2007 15 December 2007 15 December 2007

15 December 2007

  Jawabin Jagoran Juyin Musulunci na Iran    Ayatullah Sayyid Ali Khamenei   ga alhazai   a shekarar 1428 AH   December 2007   Da sunan Allah mai rahama m

 
Jawabin Jagoran Juyin Musulunci na Iran 
 
Ayatullah Sayyid Ali Khamenei
 
ga alhazai
 
a shekarar 1428 AH
 
December 2007
 
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
 
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga shugabanmu Muhammadu, zababben Allah, tare da Alayensa masu tsarki da kuma sahabbansa zababbu.
 
Aminci ya tabbabata ga masu ziyartar dakin Allah, bakin dakin Ubangiji mai alfarma, wadanda kuma suka amsa kiranSa.Gaisuwa da jinjinawa ta musamman ga wadannan da suka sabunta zukatansu da ambaton Ubangiji sannan kuma suka bude kofofin zukatan nasu domin samun shigar rahamarSa maras iyaka.
 
Akwai wadansu mutane da yawa wadanda a wadannan ranaku da darare da kuma awoyi masu tafiyar da wanzuwar rayuwa, suka zamanto cikin sanin kimar kawunansu, suka mika wuya zuwa ga Ubangiji sannan kuma ta hanyar tuba da komawa zuga Allah suka haskaka rayuka da kuma zukatansu da hasken shiriya,haka kuma suka wanke duk wata tsatsa ta zunubi da shirka a cikin igiyar ruwa ta rahmar ubangiji (S.W.T) wadda ke sauka a kowane lokaci a kan wannan wuri mai tsarki.Amincin Allah ya tabbata a kan irin wadannan zukata da ma'abotansu masu tsarki.
 
Ya kamata duk 'yan uwa, maza da mata su yi tunani dangane da wannan dama da Allah ya ba su sannan kuma su dauke ta a matsayin wata babbar dama da za su amfanu da ita.
 
Kada su yarda a nan wurin ma su shagaltu da rayuwa ta neman tara kyale-kyalen duniya, wanda shi ne abin da a kowane lokaci ke hana mu yin wani abin azo a ga ni a rayuwa. Lalle ne su zamanto sun  cika lokutansu da aiwatar da muhimman ayyuka.Su farkar da zukatansu, masu kaunar Ubangiji da shauki zuwa gare shi, daga baccin gafala ta hanyar tunawa da Allah da kaskantar da kai da komawa zuwa gare shi da kuma neman taimakonsa.
 
Nan cibiya ce ta tsantsar tauhidi na gaskiya. A nan ne Annabi Ibrahim(A.S) ya zamnto abin ambato ga duk masu kadaita bautar Allah a tsawon tarihin duniya, ta hanyar mika dansa(wanda tsoka ce daga jikinsa) domin a yi layya da shi, wanda kuma hakan ya zamanto alama ta kadaita Ubangiji da mika wuya gare shi ta hanyar yin galaba a kan son rai da kuma mika wuya zuwa ga al'amarinSa.
 
Kuma a nan ne Annabi Muhammadu,zababben Allah(S.A.A.W) ya daga tutar kadaita Ubangiji yana kalubalantar ma'abota girman kai da kuma allolin karya a zamaninsa, haka kuma ya sanya kyamar dagutu da kadaita yin imani da Allah(S.W.T) a matsayin sharadin samun tsira da rabauta:
 
(فمن يكفر باطاغوت ويؤمن بالله فقد استمسك بالعروة الوثقي)
 
(KUMA DUK WANDA YA KAFIRCE WA DAGUTU SANNAN YA YI IMANI DA ALLAH, TO KUWA LALLE YA YI RIKO DA IGIYA MARAS MAI KARFI).
 
Aikin Hajji wuri ne na sake karanta da kuma sake koyon wadannan manyan darussan (da ke tattare da wannan aya ta Alkur'ani mai girma).Yin bara'a daga mushirikai da kyamar gumaka da masu bauta musu wani ruhi ne da ke tattare da zukatan muminai.Wurare daban-daban na aikin Hajji abu ne dake yin nuni ga mika zukata zuwa ga Ubangiji da kuma yin kokari da bisa bin tafarkinSa, sannan kuma abu ne da ke yin nuni zuwa ga yin bara'a daga Shaidan da yin jifa da kuma wancakalar da shi tare kuma da yin fito-na-fito da shi.
 
Wurare daban-daban na aikin Hajji har ila yau abu ne da ke yin nuni zuwa ga hadin kan ma,bota Alkibla guda da kuma kawar da bambance-bambance na karya da gaskiya da ke tsakaninsu da fito da 'yan uwantaka da abotaka ta gaskiya kuma ta imani da ke a tsakaninsu fili.
 
Wadannan wasu darussa ne da mu musulmi daga ko'ina na duniya ya wajaba a kanmu mu koye su kuma mu sanya su a cikin tsare-tsaren rayuwarmu ta yanzu da ta nan gaba.
 
Alkur'ani mai girma ya sanya yin fito-na-fito cikin izza da makiya da tausasawa da nuna tausayi ga muminai da kuma yin bauta da kasakantar da kai ga Allah, madaukakin sarki, a matsayin abubuwa guda uku masu yin nuni ga yadda ya kamata al'ummar musulmi ta kasance: 
 
محمد رسول الله و الذين معه اشداء علي الكفار رحماء بينهم ترهم ركعا سجدا يبتغون فضلا من الله و رضوانا
 
 (MUHAMMADU MANZON ALLAH, WADANNAN DA SUKA YI IMANI DA SHI MASU TSANANI A KAN KAFIRAI, MASU RAHAMA A TSAKANINSU, ZA KA GANSU A HALIN SUJJADA DA RUKU'U SUNA MASU NEMAN FALALA DA KUMA YARDA(TA UBANGIJINSU).
 
Wadannan rukunai ne guda uku na asali wajen samun daukaka ga al'ummar musulmi.
 
Gaba dayan daidaikun musulmi ta hanyar lura da wadannan al'amara na hakika, za su iya sanin irin matsalolin da ke tattare da duniyar musulunci a halin yanzu,sani na gaskiya.
 
A yau mafiya nuna kiyayya ga al'ummar musulmi,
 
wadanda ke tafiyar da cibiyoyin  yada tunanin kasahe ma'abota girman kai, masu son kara allantuwa a kan jama'a, masu keta haddi'  suna daukar duk wata farkawa ta musulunci a matsayin wata babbar barazana ga bukatunsu na neman allantuwa a kan kasashen musulmi bisa zalunci da kaucewa doka.
 
Dole ne gaba dayan al'ummar musulmi, malamai da 'yan siyasa da ma'abota fikira da shuwagabannin jama'a a kasashen musulunci' su zamanto abu guda cikin hadin kai mai karfi kuma mai dorewa, domin bangarori daban-daban masu karfi na al'ummar musulmi su tattara karfi wuri guda domin gina al'ummar musulmi kakkarfa' mai iko.
 
Lallai ne mu san cewa neman sani da Karin ilimi da yin ayyuka cikin tsari kuma cikin tsantseni, daukan nauyin tafiyar da al'amura,dogaro ga Allah da sa buri ga samun alkawarin ubangiji,da rufe ido da kawar da kai ga barin bukatun duniya marasa kima, domin kai wa ga samun yardar ubangiji, duk su ne abubuwan asali na samun karfi ga al'ummar musulmi wadanda za su kai ta ga samun daukaka da 'yanci da ci-gaba na al'amuran da suka shafi duniya da lahira, sannan kuma su sanya makiyi ya kasa samun iya yin katsalandan a cikin al'amuran da suka shafi kasashen musulmi.
 
Nuna tausasawa a tsakanin musulmai shi ne rukuni na biyu da ke yin nuni zuwa ga yanayin da ake son al'ummar musulmi ta kasance a ciki. Kawo rabe-rabe da haifar da yakar juna a tsakanin musulmai wata cuta ce mai hadarin gasket wadda wajibi ne a yi maganinta ta hanyar yin amfani da duk wani magani da za a iya sarrafa shi wajen yin hakan.Tuntuni makiyanmu ke yin kai-kawo, ba ji ba gani wajen kawo rabe-rabe a tsakanin musulmai, kuma a wannan lokaci da muke ciki wanda a cikinsa farkawa wajen gane musulunci ta ke kara dura musu ruwa a ciki, sai kara kaimi suke yi wajen kawo cikas ga hadin kan musulmi.Abin da duk masu yi wa al'ummar musulmi fatan alheri ke cewa shi ne, bai kamata a mayar da bambance-bambance ya zamanto sabani ba ko kuma a canja yi-naka na yi-nawa zuwa yaki ba. 
 
Al'ummar kasar Iran ta yi wa wannan shekarar da muke ciki lakabi da sunan shekarar hadin kan musulunci.Sanya wannan suna ya zo ne a dalilin fahimtar da suka yi cewa makircin makiya wajen kara samar da sabani a tsakanin 'yan uwa muminai sai kara yawa yake yi.Wannan makirci kuwa ya fi karfi ne a kasashen Palasdinu da Lebanon da Iraki da  Pakistan da kuma Afghanistan, ta yadda har wani bangare na mutanen wata kasa ta musulmi suka tashi wajen yin yaki da junansu har suka zubar da jinin juna.
 
Alamomi na makircin makiya sun bayyana a cikin duk wadannan abubuwa da suka faru na ban takaici, kuma akwai idanuwa na basira wadanda daga nesa suka hangi kasamtuwar hannun makiya dumu-dumu a cikin wannan al'amari.
 
 Umarnin da alkur'ani ya bai wa mabiyansa na cewa su zamanto "MASU RAHAMA A TSAKANINSU" yana yin nuni ne zuwa ga tumbuke da kuma tono jijiyar duk  irin wadannan yake-yake daga tsakanin musulmai.
 
 A wannan lokaci na aikin Hajji kuna ganin musulmai, wadanda suka fito daga ko'ina na bangarori daban-daban na duniya kuma tattare da mazhabobi daban-daban, duk suna kewaya daki guda, suna yin salla zuwa ga dakin Ka'aba guda daya, suna yin jifan Shaidan la'ananne tare da junansu a wuri guda, a wajen yin hadaya ma suna dauke da burace-buracen zuci iri guda, a filin Arfa da kuma Mash'ar suna kaskantar da kawunansu zuwa ga Ubangijinsu tare da juna. A cikin aiwatar da wadannan ayyuka za a ga cewa mazhabobin musulunci suna da kusanci da juna ta bangaren ayyuka da hukunce-hukunce da kuma kudurce-kudurce masu yawa na asasi.Ta yin la'akari da wadannan abubuwa, za a iya tambayar cewa, to me yasa suka bar ta'assubanci da yanke hukunci bisa zato maras tushe ke kunna wutar sabani a tsakaninsu sannan kuma hannayen ha'inci na makiya masu dagula al'amura na kara rura wannan wutar a kowane lokaci?.
 
A yau wadansu marasa hangen nesa kuma masu karancin tunani na hankali, ta bin wasu hanyoyi marasa tushe suna kafirta suna kuma daukan wani babban bangare na al'ummar musulmi a matsayin mushirikai ta yadda har ma suke halatta jininsu.Irin wadannan mutane ko sun sani ko ba su sani ba, suna yin hidima ne ga shirka da kafirci da kuma ma'abota girman kai na duniya.Da yawa daga cikin  irin wadannan mutane sun kirawo  girmama kabarin Manzon Allah(S.A.A.W) da Alayensa da Waliyyai da kuma shuwagabannin addini,wanda  yin hakan girmama addini ne da kuma raya shi, sun kirawo shi da sunan shirka da kafirci, amma kuma su sun kasance suna yin hidima ne ga kafirai da azzalumai sannan kuma suna taimaka wa munanan manufofinsu.
 
Ya zama wajibi ga malamai na Allah masu son gaskiya da ma'abota fikira masu son addini da kuma shuwagabanni na gaskiya, su yi fito-na-fito da irin wannan abu mai hadari.
 
Hadin kai na musulunci a yau wani abu ne na wajibi ga mutane ma'bota hankali da tunani, wadanda zukatansu ke konuwa bisa burin ganin tabbabtuwarsa.
 
Wadannan rukunai guda biyu na daukaka: wato ta wani bangare wata iyaka ce da kuma tsaya wa a gaban duk wani irin dagawa ta duniya, ta wani bangaren kuma tausasawa da kuma taimakekeniyar abota a tsakanin musulmai, za a iya gwama su da rukuni na uku, wanda shi ne kaskantar da kai ga Ubangiji da kuma bauta masa. Al'ummar musulmi da sannu za ta sami kai waga daukaka da kuma bajinta mafi girma, kamr dai yadda musulmai suka kasance a farkon fara da'awar musulunci kuma da sannu za ta sami kubuta daga cikin ci baya na tozarta wanda aka dora a kanta ta karfi da yaji a tsawon karnonin baya-bayan nan da suka gabata.Hasken wannan motsi mai girma ya fara bullowa kuma mutane a ko'ina  cikin duniyar musulmi suna farkawa.Kafafen yada labarai da hanyoyin furofaganda na makiya da 'yan korensu sai kokari suke yi wajen ganin cewa sun danganta duk wani motsi na neman 'yanci da neman tabbatar da adalci a kowane bangare na duniyar musulmi, sun danganta shi da Iran ko kuma da Shi'anci,kuma suna dora alhakin duk wani hari da musulmai masu kishin addini daga kasashen musulmi suka kai musu ta bangaren siyasa a kan kasar musulunci ta Iran.Kasar da a karon farko ta fara daga tutar cin nasarar kafa hukumar musulunci.
 
Wadannan mutane ta hanyar yada zarge-zarge marasa  tushe a kan wasu kungiyoyi da kasashe na musulunci, kamar jarumtaka ta yakin kwanaki 33 da kungiyar hizbullah ta nuna ko kuma dagewar mutanen kasar Iraki wadda ta jawo aka kafa gwamnati da majalisar kasa da 'yan kaka-gida basu so ba ko kuwa hakuri da jajircewar ban mamaki da shar'antanciyar gwamnatin Palasdinu ta nuna tare da sadaukar da rai da mutanen kasar ke yi wajen kwato 'yancinsu, haka kuma da alamomi da yawa na sake sabunta rayuwar addinin musulunci a kasashe da dama na musulunci duk sun sanya wadannan mutane na yada zarge-zarge marasa tushe kamar cewa wai duk Iran ce ke goya musu baya ko kuma cewa wai su 'yan shi'a ne, domin kawai su hana nuna goyon bayan duniyar musulmai ga Iran din ta bangarori da dama.
 
Wannan hila da makirci kuwa ba zai iya hana sunnar Allah tabbatuwa ba, wadda ita ce samun nasarar masu yin jihadi a kan tafarkin Allah da masu kare addininSa a kan makiyansu.
 
Abin da zai zo nan gaba duk zai zama alheri ne ga al'ummar musulmi kuma daidaikunmu za mu iya kusato da abin da zai zo nan gaban ya matso kusa bisa gwargwadon ikonmu ta hanyar irin rawar da za mu iya takawa.
 
Alhazai masu alfarma, ku sani fa cewa aikin hajji wata babbar dama ce wadda za ku yi amfani da ita wajen yin shiri fiye da lokutan da suka gabata domin yin hidima ga wannan addini.
 
Ina fatan cewa taimakon Allah(S.W.T) da kuma addu'o'in Imam Mahdi, Allah Ya gaggauta fito da shi, za su taimaka muku wajen aiwatar da wannan babban hadafi.
 
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu
 
Ali khamenei
4/zul-hijja/1428
15 December 2007


| شناسه مطلب: 11400







نظرات کاربران