4 Zil-hijja 1429 4 Zil-hijja 1429 4 Zil-hijja 1429 بعثه مقام معظم رهبری در گپ بعثه مقام معظم رهبری در سروش بعثه مقام معظم رهبری در بله
4 Zil-hijja 1429 4 Zil-hijja 1429 4 Zil-hijja 1429 4 Zil-hijja 1429 4 Zil-hijja 1429

4 Zil-hijja 1429

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Qai   A wannan karon ma Qasar wahayi ta tattara dandazon muminai a baquncin da take karva duk shekara, Jama'a masu cike da qauna daga vangarori daban-daban na duniya sun taru a mahaifar musulunci da K

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Qai
 
A wannan karon ma Qasar wahayi ta tattara dandazon muminai a baquncin da take karva duk shekara, Jama'a masu cike da qauna daga vangarori daban-daban na duniya sun taru a mahaifar musulunci da Kur'ani, kuma sun shagaltu da aikin ibada wanda zurfafa tunani a kansa shi kaxai ya isa ya nuna wa xan'adam darasin dawwamar Kur'ani da musulunci wanda shi kansa mataki ne na tafiyar da rayuwa a kan Kur'ani da musulunci.
Cin nasara da rabautar xan'adam ta har abada su ne hadafin wannan babban darasin, kuma su ne hanyar tarbiyyar mutum nagari da al'umma mai nagarta, mutumin da a zuci da kuma a aikace yake bauta wa Allah shi kaxai, kuma yake tsarkake kansa daga shirka da munanan halaye da bin son zuciya, kuma yake aiki domin samar da al'ummar da ta ginu kan adalci, da 'yanci, da imani, da nishaxi, da dukkanin alamun cigaban rayuwa. 
Ayyukan Hajji suna qunshe da dokokin asali domin tarbiyyar xaixaikun mutane da al'umma. Daga lokacin sanya harami da jirkita kama da barin mafi yawa daga abubuwan jin daxi da kuma abubuwan da zuciya take so, har zuwa xawafin xakin Allah mai nuna alamar tauhidi, da salla a maqamu Ibrahim (A.S) mai rusa gumaka da sadaukarwa. Kuma da sa'ayi da sauri tsakanin duwatsu biyu (na safa da marwa) zuwa lokacin hawan dutsen ARFA a cikin taron nan mai girma na masu kaxaita Allah (S.W.T) wanda ya qunshi mutane masu launin fata daban-daban, zuwa kwana a halin zikiri da addu'o'i a filin MUZDALIFA, da kuma samun nutsuwar kowace zuciya da ubangijinta a wannan babban taron, zuwa halartar MINA da jifan Shaixan, da hadaya da take cike da ma'anar sadaukarwa ta hanyar ciyar da miskinai da 'yan tafarki, dukkan waxannan darussa ne da koyarwa da kuma tunatarwa.
Ta wani sashe a dunqule Aikin Hajji ya qunshi tsarkin zuciya da yankewa daga shagulgulan duniya, ta wani shashe kuma qoqari da qwazo da dagewa, da natsuwa da kaxaituwa da Ubangiji, da haxin kai da dunqulewa waje xaya, da sajewa da mutane; ta wani vangare kuma mayar da hankali wajen tsarkin zuciya; ta wani vangare kuma sallamawa ga al'ummar musulmi; da qasqan da kai ga Allah, da dagewa da turjewa wajen faxa da vata, da samun kai a cikin yanayi na lahira da samun qaqqarfar niyya wajen kyautata rayuwar duniya, dukkan waxannan ana aiwatar da su ne a tare kuma lokaci guda.
Allah maxaukaki yana cewa: " Kuma daga gare su akwai wanda yake cẽwa: "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu mai kyau a cikin dũniya da mai kyau a cikin Lãhira, kuma Ka tsare mana azãbar Wuta!". Baqara: 201.
Don haka ne ka'aba mai xaukaka da ayyukan Hajji suka zama madogarar al'ummu kuma qashin bayan rayuwar xan'adam kuma sun qunshi tarin riba da amfani ga mutane:
 Allah maxaukaki yana cewa: "Allah Ya sanya Ka'aba Ɗaki Tsararre, ma'aunin addini ga mutane ".Ma'ida: 97.
 Da faxinsa maxaukaki: "Dõmin su halarci abũbuwan amfãni a gare su, kuma su ambãci sunan Allah a cikin 'yan kwãnuka sanannu". Hajj: 27.
A yau fiye da kowane lokaci Musulmi daga kowace qasa kuma daga kowane jinsi ya kamata su girmama wannan babban aikin farali kuma su amfana daga gareshi, saboba damar da take gaban al'ummar musulmi tafi haske a kan kowane lokaci, kuma sanya ran isa ga hadafin da musulunci ya zayyana ga kowane mutum da kuma al'umma ya fi na kowane lokaci. Duk da al'ummar musulmi a qarni biyu da suka wuce sun ci karo da faxuwa da rushewa a gaban yammacin duniya da aqidojin qin addini daga kowane nau'i na maqiya addini da 'yan ba ruwanmu, to a yanzu a qarni na goma sha biyar na Hijira waxannan aqidojin na siyasa da tattalin arziki na yammacin duniya sun sami kafewa a laka kuma sun fara rushewa. Amma addinin musulunci a yanzu ya fara sabon zagaye na havaka da xaukakarsa ta hanyar farkawar al'ummar musulmi da dawo da qimarsu, da sake bujuro da aqidar tauhidi da taken adalci da komawa ga Allah.
Waxanda suka kasance ba daxewa ba sun yanke qauna; ba kawai suna ganin an rasa musulunci da musulmi ba ne, har ma suna ganin an rasa komawa ga Allah da riqo da addini saboda hare-haren yammancin duniya. Amma a yau sai ga shi suna ganin xaukakar musulunci da dawowar rayuwar Kur'ani da musulunci, a xaya vangaren kuma suna ganin rauni da gushewar masu yaqar musulunci sannu-sannu kuma har ma suna gaskata hakan a zuci da baki.
Tare da cikakkiyar nutsuwa ina mai cewa; wannan kawai matakin farko ne, kuma lokacin tabbatar alqawarin Allah wato cin nasarar gaskiya a kan vata, da sabunta rayuwar al'ummar Kur'ani da cigaban musulunci yana kan hanya:
Allah maxaukaki yana cewa: "Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare. Ku, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zai shugabantar da su a cikin ƙasa kamar yadda Ya shugabantar da waɗanda suke daga gabãninsu, kuma lalle ne zai tabbatar musu da addininsu wanda Ya yardar musu, kuma lalle ne Yanã musanya musu daga bãyan tsõronsu da aminci, sunã bauta Mini bã su haɗa kõme da Nĩ. Kuma wanda ya kãfirta a bãyan wannan, to, waɗancan, su ne fãsiƙai". Nur: 55.
A matakin farko alamar wannan muhimmin alqawari da ba shi da makawa shi ne cin nasarar juyin musulunci a Iran da kuma kafa tsarin addinin musulunci mai xaukaka wanda ya mayar da Iran wani sansani mai qarfi na kafuwar aqidar jagorancin addinin musulunci. Vullowar wannan al'amari mai ban mamaki ya kasance ne a daidai lokacin qololowar kirarin son duniya da qyamar musulunci na siyasar yammaci da gabascin duniya, sannan kuma tsayuwarsa qyam a gaban hare-haren tattalin arziki da siyasa da kuma farfaganda da ake yi masa ta kowane vangare, ya samar da sabon buri da sanya wani qumaji a zukatan musulmin duniya. Kuma wannan dagewar zata daxu sannan wannan fatan zai qara samun tushe da izinin Allah (S.W.T). A shekara talatin da suka gabata yankin gabas ta tsakiya da yankin qasashen musulmi na Asia da Afurka sun zama sansanin wannan fafatawa mai nasara. Yunkurin musulunci na Palasxinawa da neman kafa daular Palasxinu, da cin nasarar Hizbul-Lahi a kan yahudawan sahyoniya mashaya jini; qasar Iraqi da kafa daular musulunci mai cikakken goyon bayan mutane bayan ta'annatin Saddam; Qasar Afganistan da raunin da ya faxa mata tare da rushewar kwaminisanci da gwamnatin 'yan barandansu; rushewar saqe-saqen Amurkawa na neman samun qarfi a gabas ta tsakiya da ruxun da yake cikin haramtacciyar gwamnatin sahyoniya ta Isra'ila da kuma yaxuwar kishin addini a cikin mafi yawan qasashen musulumi musamman a tsakanin matasa da masana, da cigaba mai ban mamaki na musulmi da cigaban kimiyya da fasaha a jamhuriyar musulunci ta Iran duk da takunkumin tattalin arziki, da faxuwar 'yan ina-da-yaqin Amurka a fagen siyasa da tattalin arziki, da jin xaukaka a cikin zukatan musulmin da suke rayuwa a cikin qasashen yammacin duniya, dukkanin waxannan alamu ne a fili na cin nasara da ci gaban musulunci a kan maqiya a wannan ja-inja a qarni na goma sha biyar bayan Hijira.
Ya 'yan'uwana maza da mata! wannan cin nasara kai tsaye sakamakon qoqari ne da tsarkin niyya, a lokacin da kiran Allah (S.W.T) ya fito daga harshen bayinsa ya isa kunnuwa, a wannan lokacin ne qumaji da qwazon mujahidai a tafarkin Allah yake bayyana, a lokacin da musulmi suka yi aiki da alqawarin da suka xauka tsakaninsu da Allah a wannan lokacin ne Allah yake cika musu alqawarinsa kuma ya canja musu yanayinsu.
Allah maxaukaki yana cewa: "Kuma ku cika alƙawariNa, In cika muku da alƙawarinku". Baqara :40.
Da faxinsa maxaukaki: "Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku, kuma Ya tabbatar da dugãduganku". Muahmmad: 7.
Da faxinsa maxaukaki: " Kuma lalle, haƙĩƙa, Allah Yanã taimakon wanda yake taimakon Sa. Lalle haƙĩƙa Allah ne Mai ƙarfi Mabuwãyi ". Hajj: 40.
Da faxinsa maxaukaki: "Lalle Mũ, haqĩqa, Munã taimakon ManzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, a cikin rãyuwar dũniya da rãnar da shaidu ke tsayãwa". Gafir: 51.
Har yanzu wannan matakin farko ne: Al'ummar musulmi har yanzu suna da wahalhalu a gabansu, kuma fita daga waxannan wahalhalu ba zai yiwu ba sai ta hanyar imani da ikhlasi, da kyakkyawan fata da qwazo, da hangen nesa da haquri. Kuma ba zai tava samuwa ba ta hanyar xebe tsammani da mummunan zato, ko ta hanyar halin ko-inkula da rashin himma, ko rashin haquri da gaggawa, ko munana zato ga alqawarin Allah.
Abokin gabar da aka raunata zai fito da dukkanin qwazonsa Filin daga! don haka dole ne mu yi amfani da hazaqa, da hankali, da jarumtaka, da sanin halin da ake ciki, idan muka yi haka dukkanin qoqarin maqiya zai tashi wofi. A cikin shekara talatin xin nan abokan gaba wato Amurka da Isra'ila sun yi amfani da dukkanin qwazonsu amma ba su ci nasara ba, kuma a nan gaba ma haka zai zama.
Saudayawa tsananin qwazon maqiya yana nuna alamun rauni da rashin hangen nesansu; Duba al'amarin Palasxinu da zirin Gaza da ayyukan tsananin rashin tausayi da jin qai na maqiya a can wanda a tsawon tarihi; al'ummu kaxan ne suka ga makamancinsa, wannan alamu ne na raunin maqiya a gaban qarfin hali na maza da mata da matasa da yaran da babu makami a hannunsu amma suke fito-nafito da gwamnatin Isra'ila duk da taimakon Amurka da take samu. Kuma suka yi kunnen uwar shegu da buqatun Amurka da Isra'ila na juya wa gwamnatin Hamas baya. Amincin Allah ya tabbata ga wannan al'umma mai girma da qarfin hali, mutanen Gaza da gwamnatin Hamas sun fassara mana waxannan ayoyin a fili:
Allah maxaukaki yana cewa: "Kuma lalle ne, Muna jarrabar ku da wani abu daga tsõro da yunwa da naƙasa daga dũkiya da rãyuka da 'ya'yan itãce. Kuma ka yi bishãra ga mãsu haƙuri. Waɗanda suke idan wata masĩfa ta sãme su, sai su ce: "Lalle ne mũ ga Allah muke, kuma lalle ne mũ, zuwa gare Shi, muke kõmãwa. Waɗannan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma waɗannan sũ ne shiryayyu". Baqara:155-157.
Da faxinsa maxaukaki: "Lalle ne zã a jarraba ku a cikin dũkiyarku da rãyukanku, kuma lalle ne kuna jin cũtarwa mai yawa daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku da kuma waɗanda suka yi shirki. Kuma idan kun yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, to lalle ne, wannan yana daga manyan al'amurra". Aali Imran: 186.
Cin nasarar qarshe a wannan fama tsakanin gaskiya da vata yana hannun gaskiya, kuma daga qarshe wannan al'umma ta Palasxinu da aka zalunta zata yi rinjaye kan maqiya.
Allah maxaukaki yana cewa: "Kuma Allah Ya kasance Mai ƙarfi, Mabuwãyi". Ahzab: 25.
 A yau bugu da qari, bayan rashin cin nasarar rusa gwagwarmayar Palasxinawa a fagen siyasa, duk da qaryar Amurka da kururuwar yaudara ta neman 'yanci da demokraxiyya da kirarin kare haqqin xan'adam, to akwai kuma babbar faxuwa ga Amurka tare da mafi yawan qasashen turai da ba zasu iya samun farfaxowa a cikin gaugawa ba. Qasqancin Haramtacciyar gwamnatin Isra'ila ya qara qaruwa kuma wasu qasashen larabawa ma sun rasa mutuncinsu a cikin wannan jarabawar mai ban mamaki.
Allah maxaukaki yana cewa: "Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa". Shu'ara: 228.
 
Amincin Allah ya tabbata ga bayinSa nagari
 
Sayyid Ali Husaini Khamna'i
4 Zil-hijja 1429


| شناسه مطلب: 11408







نظرات کاربران