Zul hajj 1430 Zul hajj 1430 Zul hajj 1430 بعثه مقام معظم رهبری در گپ بعثه مقام معظم رهبری در سروش بعثه مقام معظم رهبری در بله
Zul hajj 1430 Zul hajj 1430 Zul hajj 1430 Zul hajj 1430 Zul hajj 1430

Zul hajj 1430

Da sunan Allah mai rahma mai jinkai Sakon hajji na shekarar 1430 Aikin hajji wani yanayi ne na kulla alaka da ubangiji, aikin hajji wani ruwa ne mai kyau kuma maitsarki wanda zai iya tsarkakake mutum daga dukkan zubansa, sannan ya farkar da mu

Da sunan Allah mai rahma mai jinkai
Sakon hajji na shekarar 1430
Aikin hajji wani yanayi ne na kulla alaka da ubangiji, aikin hajji wani ruwa ne mai kyau kuma maitsarki wanda zai iya tsarkakake mutum daga dukkan zubansa, sannan ya farkar da mutum daga rabkana zuwa komawa ga halittarsa ta asali ta biyya ga Allah. Tube tufafin alfahri da girman kai da banbanci a mikati da sanya tufafi launi  daya yana nuni ne zuwa ga dayantakar musulmi da hadin kai a tsakaninsu ba tare da nuna bambanci ba daga dukkan fadin duniya baki daya. Taken aikin hajji yana komawa ne  zuwa fadar Allah inda yake cewa “Ubangijinku ubandiji ne guda daya don haka ku mika wuya zuwa gare shi, kuma albishir ne zuwa ga masu takwa”. Haka nan kuma aikin hajji bayan  kasantuwarsa alama ce ta kadaita Allah sannan kuma yana nuni zuwa ga hadin kan musulmi.
Al’ummar muslmi da suka zo daga bangarori guda hudu na duniya  wato gabas, yamma, kudu da arewa don nuna shaukinsu ga ka’aba da yin dawafi da ziyarar haramin manzo (s.a.w.a.) a Madina ya kamata su yi amfani da dammar da suka samu don kara dankon zuminci da ‘yan uwantaka a tsakaninsu domin magance ciwukan da suke damunsu. A yau muna ganin yadda makiya musulunci suke kara kaimi domin raba kan alummar musulmi, don haka wannan lokaci musulmi sun fi kowane lokaci bukatuwa zuwa ga hadin kai a tsakaninsu. A yau muna ganin yadda makiya suke zubar da jinin ‘yan uwanmu a sassan duniya daban-daban, kamar yadda palasndin take karkashin zalunci na yahudawan sahaniya, sannan masallacin Aksa yana cikin hadarin na cin zarahin sahaniya. Haka nan al’ummar Gaza bayan kisan gillar da suka fuskanta yanzu ma suna cikin matsanancin halin rayuwa daga yahudawan sahaniya. Haka nan Afganistan tana karkashin mamayar manyan kasashen duniya wadanda suka sanya su a cikin musiba a kowace rana, haka rashin tsaro ya firgita mutanan Iraki a kowane lokaci suna cikin tashin hankali da firgici, haka nan kisa tsakanin ‘yan uwa musulmi da yake faruwa a Yaman shima wani abun bakin ciki ne sabo da yake faruwa a duniyar musulmi.
  Al’ummar musulmi ya kamata su yi tunani da kyau kisan gilla da tashin hankali da yake faruwa a wadannan shekaru na baya a kasashen Afganistan, Fakistan da Irak daga ina ne aka haifar dashi kuma dagaina ake shirya shi. Sannan me ya sanya kafin sojojin mulkin mallaka na Amurika da kasashen yamma su zo wadannan kasashe ba mu fuskantar wadannan matsaloli? Haka nan al’ummar falasdin da labanon da suke fafataka domin neman ‘yancinsu suna kiransu da ‘yan ta’adda, alhalin muna ganin yadda suke kissan gilla ga mutanen da suke cikin wannan yanki. Kasashe yankin Gabas ta tsakiya da Arewacin Afrika kusan karni daya kenan suke fuskantar mamaya da zaluncin kasashen Engila da faransa sannan kuma yanzu suka fada hannun mulkin mallakarda danniya na Amurika. Sannan suka kwashe arzikin wadannan kasashe suka kuma dankwafar da su. Sannan suka keta musu mutunci suka kaskanta da su. A lokacin da fafatakar al’ummar musulmi ta nuna cewa lallai ba zasu amince da cigaba da wannan hali ba, sannan ruhin shahada da jihadi a tafarkin Allah suka bayyana a cikin zukatansu ta yadda ba wani abu da zai iya maye gurbinsu, sai makiya suka sake sabon salo na mulkin mallaka wanda ya bamban da wanda aka saba das hi. A yau mulkin mallaka yana bayyana ta fuskoki daban-daban  don ganin bayan musulunci da al’ummar musulmi. Suna amfani da hanyoyin yakar al’umma ta kai tsaye ta hanyar kafofin yada labarai da dukkan abin da suke iyawa. Wannan kuwa ya hada da kisa da rusawa da yada barna da bata dabi’un matasa a kasashen musulmi, da yada miyagun kwayoyi ta yadda zasu bata matasanmu, sannan da yin amfani da kabilanci da bambance- bambance da suke a tsakanin al’umma domin raba kawunansu da raunana su da haddasa gaba a tsakanin ‘yan uwa musulmi. 
Idan soyayya da kyautata zato kaunar juna a tsakakanin mazhabobi da kungoyoyin musulmi suka maye gurbi munana zato da kyamar juna wadan makiya suke fata, babu shakka a’ummar musulmi zasu  ga bayan makirci da mugun abin da makiya suke shukawa domin raba kan al’ummar musulmi, sannan kuma zasu karya kashin bayan mulkin mallakar makiya dake damuwar al’umma. Wannan kuma yana daya daga cikin mafi  muhimmancin makasudin aikin hajji.
 Don haka idan musulmi suka yi riko da abubuwan da suka hada su na daga koyarwa k ur’ani da sunna babu shakka zasu yi karfi yadda zasu su gagari wannan barazana da take fuskantar su. Jamhuriyar musulunci ta Iran bisa kowayarwar Imam khomain babu shakka sun zama misali tsakanin al’ummar muslulmi wajen tabbatar da wannan manufa, ta yadda makiya ba su samu nasara ba a Iran. Shekara talatin suna fuskantar dasisa wadda ta hada da haifar da juyin mulki da tilasta yaki na shekaru takwas tsakanin Iran da Irak, sannan da mamaye dukiyoyin Iran da suke kasashen yamma da amurika, sannan da hare-hare na kafafen yada labarai da kirkiro karya da kazafi su dangana shi ga jamhuriyar musulunci don nisantar da la’umma daga fahimtar gaskiya. Sannan da yin kokari ta kowace hanya don ganin ta dankwafar da Iran ta fuskar cigaba na ilimi da kimiyya da fasaha, kamar yadda suke himma dare da rana suga sun hana Iran yin amfani da fasahar nukiliya. Haka nan muna iya ganin yadda suka yi kokarin shiga acikin al’amarin zaben shugaban kasa da ya gudana ba da dadewa ba, amma da ikon Allah duk ba su samu nasara ba akan wannan mugun nufi na su, ta yadda ma’anar ayan nan ta ke bayyana ga al’ummar Iran, inda Allah yake cewa “Lallai makircin shaidan mai rauni ne”. Don haka duk lokacin da fafataka ta taso daga imani da himmar al’ummar musulmi, babu shakka nasara na tare da su, kuma tabewa na tare da makiya azzalumai. Nasarar da Hisbulla suka samu akan yakin kwana 33 babu shakka yana nuni ne zuwa ga wanann hakika.
 A anan wasiyyata zuwa ga mahjjata musamman malamai da masu fada a tsakani alummar musulmi wadanda suka samu dammar halaatar wannan hajji mai albarka, sannan kuma zuwa ga masu huduba a masallacin Makka da Madina ita ce, lallai ya wajaba su san mene ne aikin da ya  hau kansu a yau. Sanann su yi kokari da dukkan himmarsu suga sun fadakar da al’mmarsu dangane da dasisar makiya, sannan su kira al’ummar musulmi zuwa ga hadin kai da taimakon juna. sannan su guji dukkan abin da iya kai al’ummar musulmi zuwa ga munana zato a tsakaninsu. Sanann su tanadi dukkan karfinsu domin fito-na-fito da makiya al’ummar musulmi , da ganin bayan tushen fitina wato Amurika da Isra’il. Sanann su bayyanar da bara’arsu ga mushrikai ta hanyar Magana da aiki.
   Daga karshe ina nemawa kaina da ku rahamar Allah tare da kaskantar da kai zuwa a gare shi.
Wassakamu alaikum warahamatulla wa barakatuhu
Sayyid Ali khamna’i 
Zul hajj 1430
 
 


| شناسه مطلب: 11420







نظرات کاربران