Cikakken Fassarar Sakon Aikin Hajji Na Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Wannan Shekara Ta 1445H (1403S): Wajibi Ne Duniya Ta Barranta Daga Hannun Gwamnatin Sahyoniya Da Amurka
Cikakken Fassarar Sakon Aikin Hajji Na Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Wannan Shekara Ta 1445H (1403S): Wajibi Ne Duniya Ta Barranta Daga Hannun Gwamnatin Sahyoniya Da Amurka
بسم اللّه الرّحمن الرّحیم
.و الحمد للّه ربّ العالمین و الصّلاة و السّلام علی خیر البریّة سیّدنا محمّدٍ المصطفی و آله الطّیّبین و صحبه المنتجبین و من تبعهم باحسان الی یوم الدّین
Kiran Ibrahimi mai ratsa jiki wanda da izinin Allah yake kiran dukkan al'umma zuwa dakin Ka'aba a lokacin aikin Hajji a kowane zamani, a wannan shekarar ma ta ja hankalin al'ummar musulmi da dama daga sassa daban-daban na duniya zuwa ga wannan tushe na tauhidi da hadin kai, kuma wannan taro mai girma da daukaka ya samu halartar mutane daban-daban, kuma ya ja hankalin mutane baki da karfin ruhin addinin Musulunci zuwa ga ruhinsa gareshi.
Babban hadadden taron ibadar aikin Hajji, idan dube shi da idon basira, za’a ga cewa wani abu ne da ke sanya karfin zuciya da d sanya nutsuwa ga musulmi, kuma abin tsoro ne da kwarjini ga makiyi da masu mugun nufi.
Ba abin mamaki ba ne idan makiya da masu mugun nufi ga al'ummar musulmi suka lalata tare da sanya shakku a wadannan bangarori biyu na farillar aikin Hajji; Ko dai ta hanyar nuna bambance-bambancen addini da na siyasa, ko ta hanyar kaskantar al'amura masu tsarki da ruhiyya.
Alkur'ani ya gabatar da aikin Hajji a matsayin alama ta bauta, zikiri da kaskantar da kai, alama ta daidaiton darajar dan'adam, alama ta tsarin rayuwar dan'adam na zahiri da na ruhi, alamar albarka da shiriya, alamar kwanciyar hankali na dabi'a da sasantawa a aikace tsakanin 'yan'uwa, Kuma alamar kyama da gaba mai karfi a kan makiya.
Bisa yin la'akari da ayoyin da suka shafi aikin Hajji da yin tadabburi a kan ayyuka da ibadar wannan aiki na musamman yana nuna mana irin wadannan sirrikan da ke a cikin hadadden tsarin aikin Hajji.
Ya ku ‘yan uwa maza da mata mahajjata alhaji yanzu kuna cikin wannan fagen aiwatar da wadannan ayyukan na gaskiya da ilimi. Ku kusantar da ayyukanku da tunanin kusa da hakan, kuma ku dawo gida tare da ainihin asalin abunda kuka samo kuma kuka koya na daga waɗannan kyawawan koyarwa. Wannan shi ne abin tsaraba mai kima kuma na hakika na tafiyar Hajjin ku.
A bana, batun barrantaka ta fi na baya. Masifun da suka faru a Gaza, wadanda suka gudana a tarihinmu na wannan zamani basu da tamka, Tsagerancin gwamnatin marasa tausayi da nuna kekashewa da tabewa, duk da sahyoniyanci yana kan rushewa, ba su bar wani wuri abun la’akari ko daga kafa ga kowane mutum ko jam'iyya, gwamnati ko kungiyar musulmi ba. Ya kamata Bara’ar wannan shekara ta zamo tafice iya lokacin Hajji da Mikat, ya zamo taci gaba a kasashe da biranen da Musulmi ke rayuwa dama gaba ki Dayana duniya, sannan kuma ta watsu zuwa ga al’umma fiye da su kansu masu aikin hajji.
Wannan barrantar (Bara’a) daga gwamnatin sahyoniyawa da magoya bayanta, musamman gwamnatin Amurka, ya kamata ta nuna kanta a cikin maganganu da ayyukan al'ummomi da gwamnatoci tare da kuntata fage ga masu aiwatar da hukuncin kisa.
Irin tsayin daka na gwagwarmayar Palastinu, da al'ummar Gaza masu hakuri da ake zalunta, wadanda daukakar hakuri da tsayin daka ya sanya duniya ta yaba musu da girmama su, dole ne a tallafa musu ta kowace fuska.
Ina rokon Allah Ya ba su nasara cikakkiya kuma cikin gaggawa, kuma ina yi muku addu’a ga ku alhazai, Allah ya kuyi Hajji karbabbiya. Allah ya amsasshiya addu'ar Sayyid Baqiyyatullah (ruhuna Fansarsa) ta zamo tare da ku.
والسّلام علیکم ورحمة اللّه
Sayyid Ali Khamenei
4 Zul-Hijjah 1445
22 ga Khurdad, 1403